Chibok: Gwamnatin Borno na ziyara a UK

Image caption Borno na kara sanar da duniya kan labarin Chibok

'Yanzu haka wata tawagar gwamnatin Jihar Borno da ta hada da gwamna Kashim Shettima, na ziyara a Birtaniya.

Ziyarar dai an yi ta ne da zummar kara gaya wa duniya irin halin da ake ciki a Jihar, game da rikicin Boko Haram.

Sakataren gwamnatin Jihar Baba Ahmed Jidda ya shaidawa BBC cewa an gane 'yan matan da aka sace sama da saba'in a videon da 'yan Boko Haram suka fitar.

Gwamna Kashim Shettima ya ce Shugaban kasa Goodluck Jonathan bai tuntube shi ba sai bayan kwanaki 19 da sace 'yan matan; bayan da kasashen duniya suka fara magana akan batan 'yan matan.

Kungiyar Boko Haram dai sun fitar da videon kuma ta bukaci a yi musaya da 'yan matan da kuma 'yan Kungiyar da suke tsare a wajan Jamian tsaro a kasar.

Sai dai Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya ture batun yin musayar a 'yan kwanakin nan.

Karin bayani