Jonathan ya soke ziyara zuwa Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jonathan na fargabar zuwa Chibok

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya soke ziyarar sa zuwa Jihar Borno inda aka sace dalibai 'yan matan fiye da 200 fiye makonni hudu da suka wuce.

Da farko an shirya cewar Mr Jonathan zai ziyarci Jihar ta Borno a ranar Juma'a a kan hanyarsa ta zuwa birnin Paris domin halartar taron koli kan batun Boko Haram.

Bayanai sun nuna cewar Shugaban ya soke ziyarar ce saboda fargabar tsaro.

Tun lokacin da aka sace dalibai 'yan mata a Chibok, Mr Jonathan bai ziyarci garin ba, kuma Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima ya ce sai da aka shafe kwanaki 19 kafin Jonathan ya tuntube shi game da batun sace 'yan matan.

Shugaba Jonathan na fuskantar matsin lamba saboda kasawar gwamnatinsa wajen ceto 'yan matan, kuma ya ce ba za a yi musayar fursunonin 'yan Boko Haram da 'yan matan da aka sace ba.

A ranar Alhamis, Majalisar Wakilan Nigeria ta amince da tsawaita dokar ta-baci a jihohi uku na arewa maso gabashin Nigeria watau Borno, Adamawa da kuma Yobe.

Karin bayani