Bam ya kashe mutane a kasuwar Kenya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Alshabaab ta tsananta kai hari a Kenya

Wasu abubuwan sun fashe a wurare akalla biyu, kusa da wata kasuwa da ke Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Jami'ai sun ce mutane 10 sun rasa rayikansu a hare-haren, wasu karin jama'a kuma sun samu raunika.

An kai hare-haren ne a kusa da lardin Eastleigh, inda yan asalin Somalia ke zaune.

Wannan al'ammari dai ya zo ne a daidai lokacin aka kwashe daruruwan 'yan yawon bude ido 'yan Burtaniya daga kasar ta Kenya.

Tuni dai ma'aikatar harkokin wajen Burtaniyar ta yi gargadin cewa ana fuskantar barazanar kai hare-haren ta'addanci a kasar, musamman daga kungiyoyin dake da alaka da kungiyar al Shabaab ta Somalia.

Karin bayani