Chibok:Mahaifiyar McManus ta ce a yi sulhu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan Boko Haram ne suka kashe Chris McManus

Mahaifiyar wani dan Birtaniya da 'yan Boko Haram suka kashe ta ce tana goyon bayan musayar 'yan Boko Haram din da gwamnati ke tsare su domin ceto rayuwar 'yan mata fiye da dari biyu da 'yan kungiyar suka sace a Chibok fiye da makonni hudu da suka wuce.

Laura McManus ta ce kubutar da 'yan matan na da matukar mahimmanci.

A shekara ta 2011 ne, 'yan Boko Haram suka sace Christopher McManus kafin daga bisani su kashe shi a wani gida a Sokoto.

Kungiyar Boko Haram ta ce ba za ta sako 'yan matan Chibok ba har sai an sako mata mayakanta da ake tsare dasu.

Fiye da wata guda kenan da 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata fiye da 200 a wata makaranta da ke Chibok a jihar Borno.