Boko Haram: Shugabanni na taro a Paris

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau

Shugaba Francois Hollande na Faransa zai karbi bakuncin wani babban taro Asabar din nan a Paris, domin duba matsalar tsaron da ta damu Najeriya.

Taron zai hada Shuwagabannin kasashen Najeriyar da Nijar da Kamaru da Benin da kuma na Chadi domin duba hanyar da za a bi domin kawar da kungiyar Boko Haram.

Wakilan Amurka da na kungiyar Gamayyar Turai da kuma na Birtania, su ma za su shiga taron.

Tattaunawar dai za ta yi nazari a aikin da kwararrun da Birtania da Faransa da Amurka suka tura Najeriyar domin su taimaka a gano 'yan matan nan na Chibok da 'yan Boko Haram suka sace.

Karin bayani