Obama ya gayyaci Firai minsitan India mai jiran gado

Narendra Modi, Fira Ministan India mai jiran gado
Image caption Narendra Modi, Fira Ministan India mai jiran gado

Shugaba Obama ya gayyaci Frai ministan Indian mai jiran gado, Narendra Modi , zuwa Washington, sakamakon nasarar da jam'iyyarsa ta samu.

Shugaba Obama ya yi wa Mr Modi waya, inda ya sheda masa cewa, yana fatan ganin an samu dangantaka ta kut da kut tsakanin Amurka da India.

Kafin zaben dai, Amurka ta ci gaba da matakin da ta dauka a kan Mr Modi na hana shi takardar izinin shiga Amurkan, sakamakon rikicin kyamar musulmi da aka yi a jiharsa ta Gujarat a shekara ta 2002.

To amma kuma yanzu ma'aikatar harkokin wajen Amurkan ta ce Mr Modi ba zai fuskanci wata matsala game da shiga Amurkan ba saboda yanzu a matsayinsa na shugaban gwamnati zai samu takardar izinin shiga ta musamman.

Tun farko dai Sonia Ghandi, shugabar jam'iyyar Congress Party, wadda ta sha kaye a zaben Indian, ta ce su dai fatan da suke shi ne, sabuwar gwamnatin Mr Modi za ta kula da muradun kasar.