Bam ya kashe mutane 10 ya jikkata 70 a Kenya

Fashewar bam a Nairobi babban birnin kasar Kenya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fashewar bam a Nairobi babban birnin kasar Kenya

Wasu bama-bamai akalla biyu sun tashi a wata kasuwa da ke babban birnin Kenya, Nairobi, ya kuma hallaka mutane 10 tare da jikata 70.

Bam daya ya tashi ne a cikin wata motar bus karama, dayan kuma ya tashi ne a cikin kasuwar Gikomba.

Lamarin ya faru ne kusa da lardin Eastleigh, wanda yanki da galibi kabilun kasar ta Somalia ke aiki da zama.

Wani mutum mai suna John Gatonye ya bayyana cewa yana wurin aikinsa lokacin da ya ji fashewar, amma da yaje wurin sai na biyu ya sake tashi.

An kai hare-haren ne a lokacin da ake kwashe daruruwan 'yan yawan bude idanu na Birtania daga Kenyan.

Dama dai ofishin harkokin wajen Birtaniyan yayi gargadin cewa akwai babbar barazanar kai hari, musamman daga 'yan gwagwarmaya musulmi 'yan Somalia.