Modi ya yi addu'o'i a kogin Ganges

Hakkin mallakar hoto AP

Mutumin da aka zaba a matsayin Fryministan India, Narendra Modi, yayi addu'oi a bakin kogin Ganges, a garin Varanasi wanda wuri ne mai tsarki ga mabiya addinin Hindu da suka fi yawa a kasar.

Modi, wanda ya samu gagarumar nasara a zaben, ya kuma ziyar ci wani wurin ibada na Hindu gabanin rantsar da shi a makon gobe.

Modi ya ce dukkan magoya bayan BJP sun yi aiki tukuru wajen tabbatarda wannan nasarar.

Ya kuma yi alkawarin tsaftace kogin Ganges wanda ke da matukar muhimmanci a addinin Hindu.

Ya samu nasarar da ba'a taba ganin irin ta a fagen siyasar kasar a shekaru fiye da 30.

Ya yi yakin neman zabe mai armashi inda yayi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar

An zabe shi ne a matsayin dan majalisa mai wakiltar Varanasi.

Ya kuma taba zama gwamnan jihar sa ta Gujarat.