Switzerland: Ana Kuri'a kan albashi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya-bayannan ta nuna jama'a za su yi watsi da shirin kara albashin.

A yau ne masu zabe za su kada kuria ta ko a bullo da tsarin biyan mafi karancin albashi a Switzerland, daya daga kasashen da suka fi arziki a duniya.

Kungiyoyin kwadagon kasar na neman a amince da mafi karancin albashin ya kasance dala 25 a sa'a daya, wanda shi ne mafi yawa a duniya.

Kungiyoyin na cewa matakin abu ne da ya kamata a yi tun a baya saboda tashin kudaden haya a biranen kasar da kuma na inshorar lafiya sun kara fatara tsakanin jama'a.

Gwamnati da masu masana'antu sun ce yawan kudin da 'yan kwadagon ke bukata ya yi yawa sosai kuma zai iya cutar da harkokin kanan kasuwanci.