Biritaniya ta aika jirgi zuwa Najeriya

Biritaniya ta aika da wani jirgin leken asiri zuwa Najeriya domin ya taimaka wajen neman 'yammatan nan 'yan sakandare su fiye da 200 da 'yan Boko Haram suka kama a watan jiya.

Tuni dai dama Amurka ta soma shawagin leken asirin a Najeriya, kuma kasashe da dama sun tura kwararru zuwa can don su taimaka.

Shugabannin kasashen Yammacin Afrika, wadanda suka yi taron koli jiya a birnin Paris, sun amince su hada karfi don yaki da 'yan kungiyar Boko Haram.

Najeriya da Kamaru, wadanda galibi dangantakarsu ba karfe gare ta ba, sun amince su dinga sintiri tare da a kan iyakarsu.

Da ma su ma 'yan kasuwar Kamarun sun bayyana irin matsalar da suke fuskanta dangane bisa hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.