Bam ya hallaka mutane shida a Kano

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A baya Kano ta yi fama da hare haren 'yan kungiyar Boko Haram

Mutane shida da suka hada da wata yarinya 'yar kimanin shekaru 10 sun mutu, a wani harin kunar bakin wake da aka kai a mota a wata mashaya Sabongari da ke Kano.

Harin ya kuma jikkata mutane da dama tare da lalata wasu motoci guda biyar da ke kusa da wurin, baya ga motar dan kunar bakin.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta wuce, a titin Gold Coast da ke Sabon gari a Kano da ke arewacin Najeriya.

Ya zuwa yanzu jami'an tsaro ba su bayar da wata sanarwa ba kuma babu wanda ya fito fili ya dauki alhakin kai harin.

An kai harin ne da kwana daya bayan da Najeriya da wasu kasashe makwabtanta suka amince su yi aiki tare domin kawar da kungiyar Boko Haram.

Karin bayani