Kotun New York ta samu Abu Hamza da laifi

Sheikh Abu Hamza al-Masri Hakkin mallakar hoto .
Image caption Sheikh Abu Hamza al-Masri

Wata kotu a birnin New York na Amurka ta samu Sheikh Abu Hamza al-Masri da laifi kan wasu ayyukan ta'addanci.

A shari'ar da aka kwashe makonni hudu ana yi, masu taimaka ma alkali yanke hukunci sun sun samu Abu Hamza da laifi ne kan wasu tuhume tuhume goma sha daya, da suka hada da bada shawarwari kan sace wasu 'yan yawon bude ido turawa 1998.

Akwai kuma zargin tura wasu mutane biyu su bude sansanin horas da mayakan sa kai a jihar Oregon.

An dai ce zai iya fuskantar daurin rai da rai.