Babu ci gaba wajen gano 'yan Chibok

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu daga cikin 'yan matan Chibok da aka sace

Kwanaki talatin da biyar kenan dai tun bayan da aka sace dalibai 'yan mata a Chibok da ke Jihar Borno a Nigeria, kawo yanzu babu cikakkun bayanai game da inda aka kwana a kokarin kubutar da su.

Kungiyar Boko Haram wacce ta sace 'yan matan a cikin makarantarsu a ranar 14 ga watan Afrilu ta yi barazanar sayar da 'yan matan a 'kasuwa'.

Lamarin ya janyo kasashen duniya sun sa baki, inda Amurka da Birtaniya da Faransa da China da kuma Isra'ila suka ce za su taimakawa Nigeria wajen kokarin kubutar da 'yan matan.

Kawo yanzu 'yan mata fiye da 200 na hannun 'yan Boko Haram a yayinda fiye da 50 suka kubuta.

Ana sukar gwamnati Shugaba Jonathan da yin tafiyar hawainiya wajen kubutar da 'yan matan.

'Jirgin Birtaniya'

Image caption Jirgin 'Sentinel R 1 zai dunga aiki ne daga Accra na Ghana

Biritaniya ta sanar da cewar ta tura wani jirgin leken asiri zuwa Nigeria domin ya taimaka wajen neman 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka kama a watan jiya.

Ma'aikatar tsaron Birtaniya ta ce jirgin leken asirin mai suna 'The Sentinel R1' mai cin mutane biyar a bar filin jirgin saman soji da ke Waddinton a Lincolnshire da kusan karfe tara da rabi a ranar Lahadi.

Tuni wani jirgin Amurka ya soma shawagi a Nigeria, kuma kasashe da dama sun tura kwararru zuwa kasar don su taimaka.

Sauran manyan kasashen da suka sa hannu a cikin lamarin, sun ce za su yi iyaka kokarinsu don ganin an kubutar da 'yan matan da ransu.

'Yaki da Boko Haram'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugabannin sun cimma yarjejeniyar aiki tare domin yakar Boko Haram.

Taro kan Boko Haram da Faransa ta dauki bakunci a Paris a ranar Asabar, ya yanke shawarar yaki da kungiyar.

Taron karkashin jagorancin Shugaba Francois Hollande na Faransa, ya samu halartar shugaban Nigeria Goodluck Jonathan da shugabannin kasashen Niger da Kamaru da Chadi da kuma Benin.

A wajen taron shugaban na Faransa da kuma na Najeriya sun ce yanzu an tabbatar cewa kungiyar Boko Haram na da alaka da kungiyar Al-Qaeda.

Kasashen da suka halarci taron, sun yanke shawarar aiki tare don ganin an murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.

Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban mutane a yayinda wasu dubun dubatan suka rasa muhallansu.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Karin bayani