Boko Haram: Ghana za ta tura soji Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon shugaban Majalisar Dinkin Duniya kuma dan Ghana, Kofi Annan ya soki kasashen Afrika kan Nijeriya

Kasar Ghana ta ba da sanarwar cewa za ta tura sojoji zuwa Nigeria, domin taimaka mata wajen magance matsalar kungiyar Boko Haram.

Wani dan majalisar Ghana, Onarable Kwamna ya shaida wa BBC cewa Ghana za ta tallafawa Nijeriya da sojojin ne ta hanyar ECOWAS.

Ya kara da cewa ECOWAS na tattaunawa game da Nijeriya, kuma da zarar an samu zarafi Ghana za ta tura nata sojojin, ko da yake bai bayyana adadin sojin da za a tura ba.

Shugaban Ghana, John Mahama shi ne shugaban kungiyar ECOWAS, kuma kasarsa ce ta farko da ta bayar da irin wannan sanarwa a nahiyar Afrika.

Tuni dai kasashe kamar Amurka da Burtaniya suka tura tawagar kwararru da jiragen leken asiri Nijeriyar, domin taimakawa wajen nemo 'yan mata fiye da 200 da Boko Haram ta sace a garin Chibok na jihar Borno.