Yunwa na barazana a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kabilar Nuer na yaki da 'yan Dinka

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir ya gaya wa BBC cewa kasarsa za ta fuskanci daya daga cikin mummunan bala'in yunwar da ba ta taba gani ba, in har ba a kawo karshen rikicin da kasar ke ciki ba a yanzu.

Mr Kiir ya ce, abu ne da ke da muhimmancin gaske a ba wa hukumomin agaji damar gudanar da aikinsu ba tare da wani tarnaki ba.

Shugaban kuma ya roki abokin adawarsa watau jagoran 'yan tawaye, Riek Machar da ya yi duk abin da zai iya domin kawo karshen fadan.

Sai dai kuma shugaban ya zargi tsohon mataimakin nasa da rura wutar fadan kabilanci tsakanin kabilar Nuer da ta Dinka, ya kuma zarge shi da saba yarjejeniyar zaman lafiyar da suka kulla a Addis Ababa a farkon watan nan na Mayu.

Shugaba Kiir ya ce a yanzu ba wai magana ce ta ko mutane za su mutu ba, ko kuma a'a, sai dai a ce nawa ne za su halaka.

Karin bayani