Zargin leken asiri ta hanyar internet

Satar bayanai ta hanyar Internet
Image caption Satar bayanai ta hanyar Internet

Gwamnatin Amurka ta tuhumi jami'an sojin China su biyar da laifin leken asiri ta Internet tana zarginsu da satar shiga manhajar kamfanonin Amurka domin samun bayanan sirri na harkokin cinikayyar kamfanonin kasar.

Mataimakin Antoni janar mai kula sha'anin tsaron kasa John Carlin ya shaidawa taron manema labaru cewa masu satar asirin ta Internet sun hari fannoni da dama na tattalin arzikin Amurka.

" Yace a karon farko muna baiyana fuskoki da sunayen wadanda ke yin wannan kutse daga Shanghai wadanda kuma ke satar bayanan yan kasuwar Amurka.

Godiya ga binciken hukumar FBI da kuma namijin kokarin gudunmar yammacin Pennsylvania.

A waje guda dai Chinan ta maida martani cikin fushi kan wannan tuhuma.

Ma'aikatar harkokin waje a Beijin ta bukaci Amurka ta fayyace abin da ta kira kuskuren da Amurkan ta tafka na tuhumar jami'an."