Chibok: Jirgin Birtaniya ya lalace

Image caption Jirgin 'Sentinel R 1' zai dunga aiki ne daga Ghana

Wani jirgin leken asiri na Birtaniya da aka tura domin kokarin gano 'yan matan da aka sace a Nigeria ya lalace kuma yanzu haka yana kasar Senegal ana gyara shi.

Wannan shi ne cikas na baya-bayannan da aka fuskanta a kokarin ceto 'yan mata dalibai fiye da 200 da aka sace a Chibok da ke jihar Borno.

Fiye da makonni biyar kenan da 'yan Boko Haram suka sace daliban, inda suka yi barazanar sayar dasu a 'kasuwa'.

Ma'aikatar tsaron Birtaniya ta ce jirgin leken asirin ya samu matsala kuma ana gyara shi a kasar Senegal.

A ranar Lahadi, Birtaniya ta aika jirgin leken asiri zuwa Nigeria don ganin cewar an kubutar da 'yan matan Chibok da ke hannun 'yan Boko Haram.

Kasashen Amurka da China da Faransa da kuma Isra'ila duk suna taimakawa Nigeria don ganin an kubutar da 'yan matan.

Kasashen duniya sun hada hannun wajen ceto 'yan matan amma kawo yanzu babu wani ci gaba da aka samu a kokarin gano inda suke da kuma yadda za a ceto su.

Karin bayani