Kungiyar Seleka ta sauya tsarinta

Hakkin mallakar hoto c
Image caption Mayakan Seleka a Bangui

Kungiyar 'yan tawayen Seleka a Jamhuriyar tsakiyar Afirka ta ce ta sake tsari domin zama mai tasiri da karfin fada a ji a kan mayakanta da ke arewacin kasar.

Gwamnatin ta yi Allah wadai da matakin tana zargin kungiyar da yunkurin kafa wata fandararriyar rundunar soji domin raba kasar da kuma kwace albarkatun da Allah ya hore mata.

Wani mai magana da yawun kungiyar ta Seleka Abdoulaye Sisseine ya ce kungiyar ta samar da ingantaccen tsarin shugabanci domin tsawatarwa mayakanta.

Kungiyar Seleka ta fafata da kungiyar Anti-Balaka a kasar abinda ya janyo mutuwar dubban mutane tare da raunata wasu da dama.

Karin bayani