Bauta da ayyukan tilas na samar da $150bn

Hakkin mallakar hoto
Image caption Miliyoyin yara ne ke ayyukan tilas a duniya

Ayyukan tilas da bauta ta zamani na samar da haramtacciyar riba ta akalla dala miliyan dubu 150, duk shekara a fadin duniya.

Wani sabon bincike da kungiyar kwadago ta Duniya, ILO ta gudanar ne ya fitar da wannan kiyasi.

Shugabar sashen yaki da ayyukan tilas ta ILO, Beate Andrees ta ce, ''Mun yi mamaki sosai da muka ga alkaluman sun zarta nesa ba kusa ba kan yadda muka yi kiyasi da farko.''

Kungiyar ta ce kashi biyu bisa uku na kudaden na zuwa ne daga harkar karuwanci, kashi dayan kuma ana samun sa ne a fannin ayyukan wankau na gida da ayyukan kwadago a gona da kuma na kamfanonin gine-gine.