'Yan sanda za su kare makarantun Nigeria

Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Babban Sufeton 'yan sanda, Muhammed Abubakar

Rundunar 'yan sandan Nigeria ta sanar da shirin tsaurar matakan tsaro a makarantun kwana a fadin kasar a wani matakin kare dalibai.

Matakin na zuwa ne makonni shida bayan da aka sace wasu dalibai 'yan mata a makarantarsu da ke Chibok a jihar Borno.

A cikin wata sanarwa kakakin rundunar 'yan sanda, Frank Mba ya ce "Babban Sufeton 'yan sanda ya umurci duka kwamishinin 'yan sanda su samar da tsaro a makarantun da ke fadin kasar".

Kungiyar Boko Haram wacce ke adawa da karatun Boko ta sace dalibai 'yan mata a wata makaranta a ranar 14 ga watan Afrilu kuma kawo yanzu ba a san inda 'yan matan suke ba.

A cikin watan Fabarairu ma, 'yan Boko Haram sun kashe dalibai maza su kusan 40 a kwalejin gwamnatin tarayya da ke Buni Yadi a jihar Yobe.