Sanatoci sun amince da dokar ta-baci

Hakkin mallakar hoto davidmark facebook
Image caption Shugaban Majalisar Datijjai, Sanata David Mark

Majalisar dattijan Nigeria ta amince da tsawaita dokar ta-baci a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe da ke arewa maso gabashin kasar na karin watanni shida.

Amincewar majalisar dattijan ta yi, ya biyo bayan takardar bukatar hakan da Shugaba Goodluck Jonathan ya aike mata.

Majalisar Dattijan dai ta amince da bukatar bayan wata tattaunawar sirri da ta gudanar saboda rarrubuwar kawunan da aka samu tsakanin sanatoci kan batun.

Sanatocin sun samu rarrabuwar kawuna ne bisa dalilai na bambancin jam'iyyun siyasa da kuma bangaranci.

Tun a makon da ya wuje ne Majalisar Wakilan kasar ta amince da batun tsawaita wa'adin dokar ta-baci a jihohi uku na arewa maso gabas.

Karin bayani