An kafa dokar soji a Thailand

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojin sun ce ba wai juyin mulki ko maye gwamnati suka yi ba sun yi hakan ne kawai domin karbar ikon tsaro.

Bayan watanni na zaman dar-dar da zanga zanga hukumar sojin Thailand ta kaddamar da dokar soji, tare da bai wa kanta iko mai yawa don aiwatar da dokar.

Babban hafsan sojin kasa na kasar Prayuth Chan-Ocha shi ne ya yi sanarwar ta talabijin.

Ya ce, '' domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka da kuma hanzarta dawo da zaman lafiya cikin dukkanin kungiyoyi da bangarori, na yi amfani da sashe na biyu da na hudu na dokar soji ta 2457, in sanar da sanya dokar a fadin Thailand.''

Sai dai kuma gwamnatin kasar ta ce ba a tuntube ta ba a kan matakin sanya dokar sojin.

Thailand dai ta na fama da rikicin siyasa ne, inda har kotuna suka umarci Frai ministar da ta sauka, kuma 'yan adawa suka nemi da wata gwamnati ba zababbiya ba ta samar da wani sabon tsarin mulki.