An hana mu kai dauki Gamboru-Ngala

Sojojin Najeriya Hakkin mallakar hoto d
Image caption An dade ana zargin sojojin Najeriya da gazawa wajen kare fararen hula a kasar.

Wani sojan Najeriya a jihar Borno yayi zargin cewar a gaban idonsu 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari kan garin Gamboru-Ngala inda suka kashe mutane har 300, amma kwamandansu yaki ba su Umarnin kai dauki.

Sojan wanda muka boye sunansa ya ce ko baya ga su sojan kasa har da jirgin saman yaki ya zo yana shawagi a sararin samaniya garin a lokacin da harin ke gudana amma ba a bashi umarnin kai harin ba.

Da ma wadanda suka tsira daga harin na Gamborun Ngala sun nemi da a janye sojojin daga garin saboda a cewarsu ba su yi musu wata rana ba sa'adda harin ke gudana.

Sojan ya kara da cewa su na zargin wannan hari da aak kai na hadin baki ne, saboda rashin hana su aiwatar da aikinsu.

Haka nan 'yan kato da gora da ke aiki a cikin Gamboru Ngala sun shaida musu cewa maharan ba su zo da makamai masu yawa ba.

Sojan yace idan har manyan su ba su cire hannunsu a harkar Boko Haram ba to kuwa ba za ayi nasa ba a yaki da ake yi da kungiyar.