'Yan sandan Brazil za su fara yajin aiki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sanda na neman karin albashi a Brazil

Daruruwan jami'an 'yan sanda daga a akalla jihohi 14 a kasar Brazil za su fara yajin aikin kwana guda, da suke bukatar ayi musu karin albashi da kusan kashi 80.

Yajin aikin na zuwa ne a daidai lokacin da saura wata guda a fara gasar kwallon kafa ta zuwa a kasar.

Jihohin da abin zai sha fa sun hada da Sou Paulo da Rio de Jenairo, inda za a fara wasan kwallon kafar da kuma gamawa.

Sai dai hukumomi sun ce 'yan sanda masu binciken muggan laifuka ne kadai za su tafi yajin aikin.

Jami'an soji da suke kula da aukuwar laifuka a wasu manyan tituna da kuma jami'an 'yan sanda masu hana shige da fice a iyakokin kasar su ba za su tafi yajin aikin ba har sai bayan gasar cin kofin duniya.

Karin bayani