FA za ta haramta wa 'yan kwallo shiga caca

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sabuwar dokar za ta fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Agusta.

Daga zangon wasanni mai zuwa za a haramtawa dukkanin kwarraru 'yan wasan kwallon kafa na Ingila shiga caca kan sakamakon wasanni.

Sai dai sabuwar dokar wadda aka amince da ita wajen Babban taron Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila (FA) na shekara-shekara ranar Laraba, za ta shafi masu buga wasa a rukunin kwararru ne kawai.

A halin yanzu dai an haramta wa 'yan wasan shiga cacar ne kawai a wasannin da kulob dinsu ke bugawa.

A karkashin wannan sabon tsarin, 'yan wasan ba za su samu damar ba wasu mutane na waje bayanai game da kulob dinsu domin su yi amfani da su wurin yin caca ba.

Karin bayani