Mutane 130 ne suka halaka a harin Jos

Mutane 130 sun halaka a hare haren Jos Hakkin mallakar hoto
Image caption Mutane 130 sun halaka a hare haren Jos

A Najeriya ana ci gaba da binciken karin gawawwakin da mai yiwuwa ke karkashin baraguzai da tarkace, sakamakon tashin wasu tagwayen bama bamai a Jos, ta jihar Pilato.

Hukumomi sun ce mutane akalla 130 ne suka halaka sakamakon harin da aka kai jiya a wata kasuwa.

Babban sifeton 'yan sandan kasar, Muhammad Abubakar, ya ziyarci inda bama-baman suka fashe domin gane wa idanunsa.

Mutane na cigaba da zuwa asibitoci domin gano 'yan uwansu da basu ji duriyarsu ba.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa harin farko na kunar bakin wake ne, amma mota ta biyu da ke dauke da bam ta fashe ne mintoci kadan bayan fashewar ta farkon.

Ya zuwa yanzu dai babu wata Kungiya da ta dauki alhakin harin.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi tur da harin na Jos, babban birnin Jihar Filato, yana bayyana maharan da cewa makiya 'yancin bil Adama ne.

Hakkin mallakar hoto bbc

Majalisar zartarwar Najeriyar ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a Jos din da kuma wasu sassan kasar a 'yan kwanakin nan.

Majalisar ta bayyana hare-haren da cewar yaki ne da ya shafi al'ummar kasar baki daya, don haka akwai bukatar jama'a su taimaka a maimakon a zuba wa jami'an tsaro ido.

Karin bayani