Rasha da China sun cimma yarjejeniya kan gas

Image caption Kuma za su yi cinikayyar ne a tsawon shekaru 30 masu zuwa

Kasar Rasha ta amince ta dinga sayarwa China da iskar gas, a karkashin wata yarjejeniya ta dubabban miliyoyin daloli.

Rasha da China sun cimma yarjejeniyar iskar gas ta $ 400 biliyan.

Shugabannin kasashen biyu Xi Jinping na China da Vladimir Putin na Rasha, sun sanya hannu a yarjejeniyar a birnin Shanghai.

Masu sharhi na ganin matsalar da Rasha ta samu da kasashen yamma, game da Ukraine ne ya janyo kasar ta shiga yarjejeniya da china.

Karin bayani