Saudiyya za ta dinga bayani kan cutar mers

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cutar ta MERs na janyo mura, zazzabi mai zafi da ka iya kaiwa ga mutuwa

Ministan kiwon lafiya a Saudi Arabia ya shaida wa BBC cewa kasar zata dinga bayyani, kan yadda take tafiyar da batun cutar Mers mai saurin kisa.

Fiye da mutane 170 ne dai suka mutu a sanadiyyar kamuwa da cutar.

Haka zalika ana samun karuwar wadanda suke kamuwa da cutar, cikin sauri a watanni biyu da suka wuce.

Har yanzu masana kimiyya basu san yadda kwayar cutar ke bazuwa ba, balle daga inda ta samo asali ba.