Boko Haram: Malamai 170 sun mutu a Borno

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Boko Haram ta kashe malamai a harin da ta kai a makarantar Buni-Yadi a jihar Yobe

Kimanin malaman makaranta fiye da 170 ne suka rasa rayukansu, a hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa a jihar Borno da ke Nigeria.

Reshen kungiyar ta jihar Borno ce ta shaida wa BBC hakan a Abuja.

Lamarin da ya jefa malaman makaranta cikin tsoro, yayin da wasu ma ke tunanin barin aikin malanta.

Kungiyar ta ce alkaluman jimilla ne na malaman da suka mutu a jihar, tun lokacin da kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hari a shekarar 2009 zuwa yanzu.