Amurka ta yi tur da harin Jos da na Kano

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry

Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya yi Allah wadai a kan fashewar bama-bamai da ya faru a Jos a ranar 20 ga watan Mayu da kuma harin da aka kai a Kano a ranar Lahadi.

Sanarwar da ofishin ya fitar, ta ce hare-hare kan fararen hula da kuma sace 'yan mata dalibai fiye da 200 a Chibok wata alama ce da ke nuna cewar bata gari za su ci gaba da gudanar da mummanan aiki.

Harin da aka kai a Jos din ya janyo mutuwar mutane kusan 118 da kuma jikkatan wasu da dama.

Sanarwar ta kara da cewar ta samu rahotanni kan zaman zullumi a Jos, kuma ta yi kira ga jama'a sun kwantar da hankalinsu.

Amurkar kuma ta ce za ta ci gaba da taimakawa Nigeria da al'ummarta a kokarin shawo kan ayyukan masu tsatsaurar ra'ayi da ke tada hankali.

Karin bayani