'Yan bindiga sun kashe mutane 25 a Borno

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu mazauna garin sun tsere Kamaru, yayin da wasu suka kwana a daji

Rahotanni daga jihar Borno a Nigeria sun ce mutane fiye da 25 sun mutu, a wani harin da 'yan bindiga suka kai garin Chikongudo.

Da yammacin ranar Laraba ne maharan suka shiga garin a kan babura da motoci, kuma dauke da bindigogi.

Mazauna garin sun ce 'yan bindigar sun kona galibin gidajen dake garin da ba shi da nisa daga Gamboru Ngala.

Wani Mazaunin kauyen ya shaida wa BBC cewa, babu dakaru a garin lokacin da lamarin ya auku.

Karin bayani