Chibok:An gyara jirgin Birtaniya da ya lalace

Image caption Kawo yanzu ba a san inda aka boye 'yan matan ba

Jirgin leken asirin Birtaniya wanda ya lalace a kan hanyarsa ta taimakawa wajen gano 'yan matan da aka sace a Nigeria, a yanzu ya isa Ghana.

Jirgin leken asirin mai suna 'RAF Sentinel' ya sauka a kasar Senegal saboda 'yar matsalar da ya fuskanci inda aka gyara shi.

Bayan kamalla gyaran a yanzu jirgin ya isa birnin Accra inda daga nan ne zai dunga tashi zuwa Nigeria don kokarin ceto 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka sace.

Wata majiya a ma'aikatar tsaron Birtaniya ta shaidawa BBC a yanzu jirgin zai soma aiki tare da jami'an Nigeria da na Amurka don gano inda aka boye 'yan matan na Chibok.

Fiye da makonni biyar kenan da 'yan Boko Haram suka sace dalibai 'yan mata fiye da 200 a makarantarsu da ke Chibok a jihar Borno.

Karin bayani