An kai hari a wata kasuwa a China

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An kai hari wata kasuwa a China

Kafar yada labaran China ta rawaito cewa an kai hari a wata kasuwa da ke bakin hanya kusa da wurin shakatawa na Orumchi,a yammacin yankin Shinjang.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya ce mutanen da ba a san adadin su ba sun rasa rayukansu a harin.

Motoci ne suka kutsa cikin jama'a a kasuwar ka na suka fara jefa ababen fashewar, nan take daya daga ciki ya tashi da mutanen kasuwar.

Hukumomin China sun sha zargin masu tsattsauran ra'ayi da kai hare-hare da kuma jefa bam akan wasu masu tada kayar baya 'yan aware a yankin, wurin da 'yan kabilar Wiga suka fi zama kuma yawancinsu musulmai ne.

Karin bayani