Faransa ta nemi a dakatar da fada a Kidal

Wasu Azbinawa rike ta tutarsu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sabon fadan na neman kawo karshen yunkurun sasantawa da Azbinawa na kungiyar MNLA

Kasar Faransa ta yi kira da a kawo karshen fadan da ake yi a arewacin Mali nan take.

Hakan na zuwa ne bayan 'yan tawayen Azbina sun fatattaki dakarun gwamnati a garin Kidal.

Wani kakakin 'yan tawayen ya ce sun kashe sojojin gwamnati da dama, kuma sun kama wasu.

Gwamnati ta amince cewa dakarunta sun janye daga garin, kana shugaban kasar ya nemi a tsagaita wuta ba tare da bata lokaci ba.

A ranar Asabar da ta gabata ne fada ya barke, lokacin da Firai minista Moussa Mara ya kai ziyara Kidal, domin nuna kwarin gwiwa ga dakarun da ke can.

Karin bayani