Hari a hedkwatar PNDS-Tarayya a Yamai

Shugaba Mahamadou Issoufou Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar wani hari da aka kai a cibiyar jam'iyar PNDS Tarayya mai mulki ya jikkata wasu mutane uku.

A halin yanzu mutanen suna kwance a asibiti ana yi musu magani.

Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga tantance wadanda suka kai wannan harin ba a birnin Yamai.

To amma hukumomin 'yan sanda sun kaddamar da bincike.

Hakan ya biyo bayan wani harin da wasu mutanen dauke da makamai da ba a san ko su wanene ba, suka kai a gidan mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Ben Omar Mohamed.

A makonnin baya ma an kai hari a gidan shugaban majalisar dokokin Nijar din Malam Hama Amadou.

A yanzu haka dai ana fama da rikicin siyasa tsakanin jam'iyyu masu mulki da 'yan adawa.