Sojoji sun yi juyin mulki a Thailand

Image caption Manyan sojojin kasar a lokacin sanarwar juyin mulki.

Babban hafsan sojin kasar Thailand, Janar Prayut Chan-O-Cha ya sanar a gidan talabijin kasar cewar sojojin sun kwace mulkin kasar.

A cewarsa zai gudanar da sauye-sauyen siyasa.

A ranar Talata ne dakarun kasar suka sanar da dokar ta baci.

Janar din ya gayyaci 'yan siyasar da ke hammaya da juna don warware takkadar da ke tsakaninsu amma sai suka kasa cimma maslaha.

A yanzu haka dai jami'an soji sun zagaye gidan da shugabannin siyasar kasar ke tattaunawa domin daidaito tsakaninsu.

Karin bayani