Chibok: Kungiyar NMFUK ta yi Allah wadai

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar Al'ummar Musulmin Nigeria da ke Birtaniya watau NMFUK ta yi Allah wadai da ayyukan 'yan Boko Haram a Nigeria musamman sace 'yan mata dalibai a Chibok na Jihar Borno.

A cewar kungiyar, ayyukan Boko Haram sun saba da koyarwar addinnin Musulunci saboda babu wata hujja da 'yan tada kayar bayan suke da ita a cikin Alkur'ani ko Hadisi.

Sanarwar da mai magana da yawun kungiyar ta NMFUK, Dr Musa Aliyu ya fitar, ta bukaci gwamnatin Nigeria ta matsa kaimi wajen kokarin ceto 'yan matan sannan a mika su wajen iyayensu.

Kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya su matsa lamba kan Nigeria domin ta bada fifiko ga matakan kare lafiya da dukiyoyin al'umma, saboda galibi talakawa ne ke afkawa cikin masifa sakamakon ayyukan Boko Haram.

Fiye da makonni biyar kenan da 'yan Boko Haram suka sace dalibai fiye da 200 a Chibok, kuma shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya yi barazanar sayar da 'yan matan a 'kasuwa'.

Karin bayani