'Shugabanin Afrika ku magance matsalarku'

Shugaban  Rwanda Paul Kagame Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Kagame yace shugabannin Africa sun gaza wajen magance matsalolin da suka addabi yankin.

Shugaban Rwanda Paul Kagame ya kalubalanci shugabannin Afrika, da su rungumi nauyin da ya rataya a kansu kuma su karbi gazawarsu.

Shugaban ya yi shagube ne kan ziyarar da wasu Shugabannin Kasashen nahiyar suka yi zuwa kasar Faransa, inda suka gana da Shugaba Francois Hollande domin shawo kan matsalolin tsaro a nahiyar.

Inda ya ce yawancin shugabannin sun je ne domin daukar hoto da shugaban Faransa, wanda hakan ka iya janyowa a yiwa nahiyar wani duba na daban.

Shugaban Najeriya ma Goodluck Jonathan ya halarci wannan taron.

Shugaba Kagame ya kara da cewa kamata ya yi shugabannin Afrika su taru, domin tattauna matsalarsu tare da ba juna shawarar yadda za su magance ta.

Karin bayani