Duniya ta kyamaci juyin mulkin Thailand

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Juyin mulkin Thailand bai sami karbuwa ba

Kasashen duniya sun yi Allah-wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Thailand.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce babu dalilin yin juyin mulki.

Shi ma sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-Moon ya yi kiran da a gaggauta dawo da Dimokradiyya kasar; kamar yadda mai magana da yawunsa Stephane Dujarric ya shaidawa BBC.

A bangare guda kuma gwamnatin Sojin kasar ta bukaci tsohuwar Firai-Minista Yingluck Shinawatra da masu fada a ji a harkokin siyasar kasar da su bayyana a gabanta.

Karin bayani