Fafaroma na ziyara a Gabas ta tsakiya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fafaroma na ziyara a Gabas ta Tsakiya

Fafaroma Francis zai isa kasar Jordan a yau Asabar don fara wata ziyara ta kwanaki uku a yankin Gabas ta tsakiya.

Fafaroman ya ce za a yi ziyarar ne don kokarin samar da sabuwar dangantaka tsakanin mabiya addinin Kirista masu bin tafarkin orthodox; bayan da aka shafe shekaru dubbai ba a ga maciji da juna.

Sannan kuma za ai addu'o'i a bainar jama'a da babban Malamin Adidinin kirista masu bin darikar orthodox.

Ana tsammanin Fafaroman zai yi amfani da karfin ikonsa da Shugabannin siyasa a Israela da kuma Yankin kogin Jordan don rage tashin hankula a yankin.

Karin bayani