An kai hari majalisar dokokin Somaliya

majalisar dokokin somalia
Image caption majalisar dokokin somalia

Akalla mutane goma ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai a kan majalisar dokoki a Mogadishu, babban birnin kasar Somalia.

Rahotanni sun ce 'yan bindiga dauke da manyan makamai ne suka diran ma ajalisar bayan an ji fashewar bom din da aka tada a kofar shiga ginin majalisar. An ji amon bindigogi bayan fashewar.

'Yan majalisar da ke cikin ginin yayin da aka kai harin, an sami kwashe su daga wurin.

Ana jin 'yan siyasa biyu suna cikin wadanda suka sami raunuka.

Wani dan siyasa ya fada wa BBC cewa ana ci gaba da ba-ta-kashi.

An tura sojin Tarayyar Afrika da na Somalihyar zuwa wurin.

Kungiyar Al-Shabab mai alaka da Alka'ida ta ce ita ce ta kai harin.