Za a rantsar da Jacob Zuma a yau Asabar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jacob Zuma zai yi wa'adi na biyu

Nan gaba a yau ne za a rantsar da shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma a karo na biyu a birnin Pretoria.

A ranar Laraba ne dai 'yan majalisar kasar suka zabe shi wadanda suka mamaye zaben kuma yawancinsu 'yan jami'iyyarsa ta African National Congress ne.

Jam'iyyar ANC ta yi nasara da kuri'u fiye da kashi sittin da biyu a zaben da aka gudanar farkon wannan watan .

Wannan shi ne karo na biyar da jam'iyyar ANC ke samun nasara a kasar ta Afrika ta Kudu tun bayan mulkin wariyar launin fata.

Karin bayani