An kashe mutane 24 a Jihar Borno

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya wasu 'yan bindiga sun kai tagwayen hare hare a Jihar Borno dake arewa maso gabacin kasar, inda suka kashe akalla mutane 24.

Maharan wadanda ake zaton 'yan Boko Haram ne sun harbe mutane a kauyen Kamuya dake Karamar Hukumar Biu ta Jihar Bornon.

Mazauna wajen sun ce maharan sun shiga kauyen ne a kan babura dauke da bindigogi, suka kuma tare hanyar shiga kauyen suka yi ta harbin mutane.

An ce a yanzu haka dai mutanen kauyen sun gudu saboda fargabar sake kai musu wani harin.

Wani mazaunin kauyen ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa ya kirga gawawwakin mutane 24 da aka kashe.

Haka kuma an harbe wasu yara a garin Warabe a wani harin da aka kai masu.

Babu dai cikakken bayani yawan yaran da aka kashe a can.

Hukumomi basu ce komai ba akan wadannan hare haren.

Jihar Borno na daga cikin jihohi ukku dake karkashi dokar ta-baci, wadda aka kafa tun bara saboda hare haren 'yan Boko Haram -- sauran jihohin biyu sune Yobe da Adamawa.

'Yan Boko Haram, wadanda suka kame 'yan mata fiye da 200 daga makarantar sakandare ta Chibok dake Jihar Bornon, suna da karfi sosai a jihar.

Karin bayani