Belgium: Matakan tsaro a wuraren Yahudawa

Gidan ajiyar kayan tarihin Yahudawa a birnin Brussels Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gidan ajiyar kayan tarihin Yahudawa a birnin Brussels

Hukumomi a Belgium sun tsaurara matakan tsaro a wuraren ibadar Yahudawa bayan harin da aka kai gidan ajiyar kayan tarihin Yahudawan.

Wani da dan bindiga-dadi ne ya bude wuta a wurin ajiyar kayan tarihin dake birnin Brussels, ya kuma hallaka mutane 3 da raunata mutum na hudu.

Bayanai sun ce ya fito ne ya kuma fara harbin kan mai uwa da wabi kan mutane a daidai mashigin wurin, kana ya dawo ya ja motarsa ya gudu.

Prime Ministan kasar ta Belgium Elio Di Rupo ya ce, kan kasar sa a hade yake wajen kalubalantar abinda ya kira harin na Mugunta.

'Yan sandan kasar ta Belgium sun ce sun damke wani da ake zargi wanda ya tsere daga yankin, suna kuma neman karin wani mutumin.

Prime Ministan Isra'ila Binyamin Netanyahu ya yi Allah Wadai da harin a matsayin tsokanar da ake cigaba da yi ma Yahudawa da kasar su.