Nigeria ta dakatar da musayar 'yan Chibok

Hakkin mallakar hoto AFP

Wata jaridar Burtaniya ta wallafa labarin cewa saura kiris a yi musayar 'yan matan Chibok da mayakan Boko Haram, amma gwamnatin Nigeria ta dakatar da hakan.

Jaridar Daily Mail ta ce, da alama dakatar da musayar 'yan matan ya fusata shugabannin kungiyar ta Boko Haram.

Bayanai sun ce shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya yi waya cewa a dakatar da musayar, daga birnin Paris inda ya halarci wani taro kan batun tsaro tare da shugabannin kasashe makwabta da kuma shugaban Faransa.

Jaridar ta ce wani ne da kungiyar ta amince da shi, ya zama mai shiga tsakanin kungiyar da gwamnatin Najeriyar, a kokarin ceto 'yan matan cikin ruwan sanyi.

Daily Mail din ta ce, mutumin ya yi tafiya mai cike da hadari, inda ya je sansanin 'yan kungiyar Boko Haram ya kuma samu amincewarsu na su sako 'yan matan da suka sace a garin Chibok, yayin da kuma za a sako musu wasu daga cikin magoya bayansu da gwamnati ke tsare dasu.

Hakkin mallakar hoto AP

A cewar bayanan mutumin ya ga 'yan matan da aka sace da idonsa, kuma tabbatar da cewa ana ciyar da su da kula da su yadda ya kamata, kuma 'yan matan na Chibok, sun shaida masa cewa suna son gwamnatin Nigeria ta biyawa 'yan kungiyar bukatunsu, domin su koma gidajen iyayensu.

Sai dai ana daf da cimma yarjejeniyar fara musayar 'yan matan Chibok din ne gwamnatin Najeriya ta dakatar da hakan.

Bayanai sun nuna cewa kwan-gaba kwan-baya da gwamnatin Najeriya ke yi game da hanyoyin da za a bi, wajen kwato 'yan matan fiye da 200 ne ya janyo soke shirin ceto 'yan matan ta hanyar musaya.

A ranar 17 ga watan Mayun da muke ciki ne, Shugaban Faransa Francios Hollande ya kira taro kan batun tsaro a Paris, inda shugaba Jonathan ya gana da shugabannin kasashen Nijar da Kamaru da Chadi da kuma jami'an diflomasiyyar Burtaniya da Amurka da Israila da kuma Faransar.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugabannin sun amince su hada karfi waje guda wajen magance matsalar tsaro a Nigeria