'Za a yi zaben 2015 duk da rashin tsaro'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana sukar shugaba Jonathan saboda gazawa wajen tabbatar da tsaro a Nigeria

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan, ya ce za a yi babban zabe a shekarar 2015, duk da matsalolin tsaro da kasar ke fama da su.

Shugaba Jonathan ya fadi haka ne a wani jawabin da ya yi a wani coci a Abuja, inda aka gudanar da addu'oin zagayowar 'Ranar Dimokaradiyya'.

Mista Jonathan ya ce ana kai hare-haren ne da zummar durkusar da gwamnatinsa, inda ya kara da cewa kasar za ta shawo kan matsalolin tsaron da ke addabarta duk da cewa sai suna kara kamari.

'Yan adawa da ma 'yan kasar da na kasashen waje na ci gaba da sukar shugaba Jonathan, saboda gazawarsa wajen shawo kan matsalolin tsaro, musamman hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke kai wa.

Karin bayani