An yi addu'oin zaman lafiya a Nigeria

Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sarkin Musulmi Sultan Sa'ad Abubakar Najeriya

Al'umar Musulmi a Abuja fadar gwamnatin Najeriya, sun gudanar da wasu addu'oi na musamman domin neman zaman lafiya da tsaro.

Sarkin Musumi Sultan Sa'ad Abubakar ne ya kira taron addu'ar, yana mai cewa Musulunci bai yarda da ta'addanci ba.

A makon da ya gabata ne, wani dan kungiyar kare hakkin bil-adama ya rubuta wasika zuwa ga Sarkin Musulmin, yana kira gare shi da ya kara taka rawa ta shiga tsakani da kungiyar Boko Haram.

Har yanzu dai kungiyar tana tsare da 'yan mata 'yan makaranta fiye da 200 wadanda ta sace a cikin watan Aprilun da ya gabata.