'Yan bindiga sun kashe mutane 20 a Adamawa

Gwamnan Adamawa Murtala Nyako Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kawo yanzu dai ba a san inda mazauna kauye Waga da dama suka shiga ba

Hukumomi a jihar Adamawa da ke arewa-maso-gabashin Nigeria, sun ce wasu 'yan bindiga sun kashe akalla mutane 20, a harin da suka kai kauyen Waga.

Sai dai an ce jami'an tsaro sun yi nasarar dakile harin da aka kai a kauye na biyu, Gublak da ke jihar ta Adamawa duka a karshen mako.

'Yan bindigar da ke cikin motoci da kan babura sun kona gidajen kauye na Waga da dama da kuma kayan abinci.

Mazauna yankin sun ce da safiyar ranar Lahadi ne yayin da mutanen kauyen na Waga ke ibada a mujami'arsu aka kai harin.