Tsoffin gwamnonin Akwa Ibom za su more

Gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dokar da aka sanya wa hannu ranar Litinin na janyo kace-nace

Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom da ke kudancin Nigeria ta amince da wani fansho mai tsoka ga tsofaffin gwamnonin jihar.

A karkashin sabuwar dokar za a dinga bai wa tsohon gwamna fansho daidai albashin gwamna mai ci har mutuwarsa.

Haka zalika za a bashi kudin da ba zai wuce miliyan biyar ba duk wata domin 'yan aikin gidansa.

Sannan za a bashi wata miliyan 100 duk wata, na kula da lafiya da kuma gida mai daki biyar a Abuja ko a jihar.

Bugu da kari kuma za a bashi giratuti na kashi 300 bisa 100 na ainihin albashinsa na shekara a lokacin da ya bar aiki.