Kamaru ta tura dakaru kan iyaka da Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Paul Biya, shugaban Kamaru

Kamaru za ta tura dakaru kusan 1,000 zuwa kan iyakar ta da Nigeria a yinkurin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.

Kakakin ma'aikatar tsaron Kamaru, Laftanar Kanar Didier Badjeck ya ce dakarun na tabbatar da tsaro ne kuma za su maida martani idan har aka kai musu hari.

Dakarun kuma za su dunga sintiri a yankunan arewacin kasar ta Kamaru.

A cewar Badjeck tun a watan Maris aka tura wasu sojoji 700 a lardin arewacin kasar domin yaki da Boko Haram.

A can baya Nigeria ta yi korafin cewar gwamnatin Kamaru ba ta bada hadin kai wajen murkushe ayyukan Boko Haram.

A cikin tsakiyar wannan watan ne shugabannin Nigeria da Chadi da Kamaru da kuma Niger suka tattauna a Paris, inda suka lashi takobin yaki da Boko Haram.

Karin bayani